ABNA24 : Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto shugaban kungiyar likitocin wacce ake kira NARD, wato Aliyu Sokomba yana cewa sun koma yajin aiki ne don gwamnatin tarayyar kasar ta kasa cika alkawuran da ta yi masu na biyan albashinsu, da biyan alawus na ayyuka masu hatsari da suke yi da wasu bukatun.
Dr Sokomba ya ce babu kayakin aikin kare lafiyar likitoci a asbitoci da dama a kasar. Sannan basu da inshoran lafiya, banda haka ayyukansu ma na cikin hatsari. Sannan bugu da kari, wasu gwamnoni a jihohin kasar sun kasa biyan likitoci albashinsu.
Daga karshe shugaban kungiyar likitocin ya ce, likitocin suna fama da wannan matsalar tun shekara 2017.
Amma ‘yan sa’o’ii kadan bayan da likitocin suka fara yajin aiki a jiya Litinin, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa likitocin ba su da hujjar sake komawa yajin aiki, don an biya mafi yawan bukatunsu.
Ministan kwadago Mr Chris Ngige ya bayyana cewa tuni gwamnatin tarayyar ta warware bukatunsu guda 6 cikin daga cikin 8 da suka gabatar.
342/